News

Jami’an Tsaro Sun Cafke Wani Matashi Da Laifin Sare Hannayen Mahaifiyarsa Mai Shekaru 65 Da Adda

Jami’an Tsaro Sun Cafke Wani Matashi Da Laifin Sare Hannayen Mahaifiyarsa Mai Shekaru 65 Da Adda

Jami’an ‘yan sanda sun kama wani matashi da ake zargi da sare hannayen mahaifiyarsa mai shekaru 65 tare da yi mata mummunan sara a kanta, sannan ya yayyanke ta a kafarta da wasu sassan jikinta.

Idon Mikiya ta rawaito cewar, wanda ake zargin ya yi wa datijuwar wannan aika-aika ne a ƙauyen Akibo da ke ƙaramar hukumar Obafemi Owode ta Jihar Ogun.

A cikin daren ranar Laraba ne aka ji hayaniya a gidan tsohuwar, inda makwabta suka je domin kai ɗauki, amma ko da suka isa, sai suka same ta cikin jini, da hannuwanta biyu duk an datse su, da kuma sara a kanta, shi kuma ɗan nata yana tsaye a kanta ya rike wata sharɓeɓiyar adda.

Jaridar Punch ta bayyana wani maƙwabcinsu yana cewa wanda ake zargin ya kuma sari mahaifiyar tasa a ƙafa da wasu sassan jikkinta, amma an kaita asibiti domin ba ta kulawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce rundunarsu ta cafke matashin kuma sun fara gudanar bincike kan lamarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button