News

Jami’in Agaji Yayiwa Yarin Yar Sbekara 17 Fyade, Har Saida Ta Kashe Kanta Da Kanta Saboda Takaici

Jami’in Agaji Yayiwa Yarin Yar Sbekara 17 Fyade, Har Saida Ta Kashe Kanta Da Kanta Saboda Takaici

Rundunar ‘yan sanda a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce tana ci gaba da bincike kan wani ma’aikacin agaji da ta kama bisa zargin ya yi wa wata matashiya ‘yar gudun hijira fyaɗe a Maiduguri.

An kuma yi zargin cewa matashiyar ta kashe kanta bayan faruwar lamarin a unguwar rukunin gidajen 303 ranar Talata.

‘Yan sanda ne dai suka kai dauki lokacin da suka jiyo ihu da kuma hayaniyar matashiyar ‘yar kimanin shekara goma sha bakwai.

Sun ce bayan bude kofa ne kuma sai matashiyar ta fito tana korafin cewa an keta mata matancinta.

Wannan Matashiya Dake Sansanin Gudun Hijira A Maiduguri Ta Kashe Kanta Saboda Takaicin Fyaden Da Wannan Matashi Ya Yi Mata

Rahotanni sun nuna cewa marigayiyar ta fita yawon aikatau ne domin neman na abinci a matsayin ta na ‘yar gudun hijira, inda bayan ta je aiki gidan matashin ne ya yi amfani da wannan dama ya yi mata fyade, inda ita kuma bakin cikin hakan ya sa ta ruga a guje ta shiga kicin dinsa ta dauki wuka ta burmawa kanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button