Kannywood News

Jarumin Cikin Shirin Fim Din Kwana Casa’in Sahabi Ya Samu Karuwar Da Namiji

Jarumin Cikin Shirin Fim Din Kwana Casa’in Sahabi Ya Samu Karuwar Da Namiji

‘Sahabi’ Ya Samu Karuwa Da Da Namiji

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood a arewacin Najeriya, Ali Hussein, wanda aka fi sani da Sahabi a shirin Kwana Casa’in na Arewa 24, ya samu karuwa da da namiji.

Jarumin ne ya wallafa labarin a shafinsa na Instagram yana mai nunawa godiyarsa ga Allah.

“Allah ya azurta ni da samun da namiji.” Tuni dai har ya radawa dan suna.

“Allah ya raya #Ramadan, Alhamdulillahi, yaro ina maka maraba da zuwa duniya.” In ji jarumi Hussein, wanda  ke fitowa a shirin na Kwana Casa’in mai dogon zango a matsayin dan jarida.

An dai ga jarumin ya wallafa wani dan takaitaccen bidiyon jaririn wanda aka rangadawa ado.

Shi kuma a daya gefen ya saka tufafi na Larabawa yana murmushi har da saka tabarau –  wani abu da ke nuna yana cikin yanai na farin ciki.

Tuni abokanan sana’ar jarumin da masoyansa suka yi ta tururuwar taya shi murna.

“Allah ya raya” In ji jaruma Saratu Doso.

“Allah ya raya Ramadan.” Umar Abdullahi ya ce.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button