News

Karshe Da Ajalin Dan Fashin Daji Bello Turji, Daga Datti Assalafy

Karshe Da Ajalin Dan Fashin Daji Bello Turji, Daga Datti Assalafy

ABINDA YAKE FARUWA TUN ASALI

Idan zaluncin mai zalunci yayi tsanani tabbas yana dab da zama tarihi ne,

Babu wani azzalumi ‘dan ta’adda a tarihin duniya wanda ya wuce shekara 10 sau biyu a duniya yana aikata kisan kai da fyade wa mata bai zama tarihi ba

Da kuka ji sunan shugaban ‘yan ta’adda na Arewa maso yamma Bello Turji ya karade ko’ina ana ta masa bakar addu’ah to alamace dake nuna yana dab gushewa kamar magabatansa

Idan ta tabbata samamen da sojoji suka kai masa har sansaninsa a shekaran jiya basu murkushe shi ba, to ba makawa tasa ta kare, zai cigaba da ci baya kenan har a wayi gari ya zama tarihi

Bello Turji ko yana raye ba zai sake tasiri ba kuma, domin yanzu haka sojojin Nigeria sun kafa tutar Nigeria a sansaninsa

Yaa Allah Ka kara wa Bello Turji kaskanci, Ka bashi dacewa da mutuwar wulakanci

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button