Kannywood News

Wata Sabuwa: Jarumin Kannywood Sadik Sani Sadik Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Wasu Laifuka Da Ake Karar Jarumin

Jarumin Kannywood Sadik Sani Sadik Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Wasu Laifuka Da Ake Zarginsa Da Aikatawa

Daga Indabawa Aliyu Imam

Kotun shari’a da ke unguwar Hotoro masallacin juma’a a birnin Kano za ta saurari karar da aka shigar kan Jarumin masana’antar Kannywood Sadiq Sani Saniq bisa zargin ruf da ciki kan kudaden wani bawan Allah.

Aliyu Muhammad Hanas wanda Darakta ne kuma Furodusa a masana’antar shirya fina-finan hausa, ya shigar da korafin Jarumi Sadiq Sani Saniq cewa yana bin sa kudade amma Jarumin ya ki ya biya shi, ya kuma yi masa alkawari fiye da shurin masaki bai biya ba, karshe ma sai ya daina d’aukan wayarsa.

“Na tuntubi Gambo (Sadiq Sani Sadiq) kan wani fim da nake so ya fito min a ciki, mun yi ciniki da shi na dakko kudi na ba shi, sai aka sami matsala bai zo ba, na d’aga lokacin aikin nan ma bai zo ba, karshe dai na nemi Ali Nuhu ya maye min gurbinsa, daga baya ne na nemi ya dawo min da kudina amma sai ya yi ta min wasa da hankali.” Cewar Furodusa Aliyu Hanas.

“Akwai sanda na sami labarin yana cikin shoprite Kano, na d’auki ‘yan sanda muka tafi don hukuma ta tirsasa shi ba ni hakkina, a lokacin ne ya ba ni wani abu daga kudin, ta hannun Maje Elhajeej Hotoro.

Furodusa Usman Muazu ya yi kokarin shawo kansa ba shi ka’dai ba, har da su Alasan Kwalle da su Sulaiman Abubakar amma bai ba ni kudina ba. Don haka na maka shi a Kotu don a yi mana shari’a ya dawo min da hakkina.” In Ji Darakta Aliyu Hanas.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button