E/News

Labari mai dadi : Kamfanin BUA ya shirya rage kudin siminti

Labari mai dadi : Kamfanin BUA ya shirya rage kudin siminti

Wannan labari ne Mai dadi. A saboda haka ake son a sami abokin hamayya a kasuwanci.

Kuma ga dalilin da ya sa mutane su daina yin shiru a kan abu. A yanzu ga shi an sami sauki.

Kamfanin siminti na BUA karkashin jagorancin Alhaji Abdussamad Rabiu ya yi alkawarin rage farashin siminti a fadin kasar Rabi’u ya bayyana haka ne yayin babban taron kamfanin karo na bakwai a jiya Alhamis 31 ga watan Agusta a Abuja.jaridar legit na tattaro wannan labari.

Ya ce zai samar da wadataccen siminti a kasar don samun damar rage farashin madadin shirin gwamnati na fara shigo da shi

cewarsa:

“Zuwa karshen wannan shekara mu na fatan kara samar da siminti a kamfanonin mu guda biyu don kara yawan siminti da mu ke fitarwa da kaso 40.

“Hakan zai taimaka wurin samun wadataccen siminti zuwa tan miliyan 70.

“Dalilin kara yawan samar da simintin shi ne don rage farashin madadin shigo da shi kasar wanda hakan ba alkairi ba ne.”

Meye BUA ya ce kan shigo da saminti?

Ya kara da cewa a yanzu farashin siminti ya kai Naira 4,500 wanda hakan ke nuna tan daya ya kai Naira 90,000 kenan ko kuma Dala 100.

Idan kuma gwamnati ta ce za ta fara shigo da shi kasar, to hakan zai kara farashin ne ba ragewa ba duba da abubuwan da su ke ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button