Uncategorized

Mahaifin Daya Daga Cikin Matan Da Akai Garkuwa Dasu Ya Rasu

Allah yayiwa mahaifin daya daga cikin daliban makarantar Federal College of Forestry Mechanisation, Ta Jahar Kaduna Da Aka Sace.

Mahaifin Daya Daga Cikin Daliban Mai Suna Alhaji ibrahim shamaki Mahaifin fatima ibrahim shamaki

Ana kyautata zaton mutuwar tasa nada nasaba da rashin lafiyar da yakamu da ita tun bayab sace yarsa da akai a makarantar kamar yadda lauyansa Farfesa Chidi Odinkalu Ya Sanar A Shafinsa na twitter.

Fatima dai na cikin dalibai 39 da suka fada cikin iftila’in garkuwa da ake zargin yan bindiga da yi a jahar kaduna.

Tabbas lamarin garkuwa da dalibai na cigaba da bawa iyaye tsoro musamman ma a yankin arewacin nigeria

Wanda hakan ke tilasta gwamnati rufe wasu makarantun

Har yanzu gwamnati bata ceto daliban ba lamarin sa yasa wasu qungiyoyi gami da dai daikun jama’a yin zanga zangar tilasta gwamnatin ceto rayuwar daliban

Andaiji gwamnan kadunan na shelnta cewar bazai shiga zaman sulhu da yan ta’addaba

Lamarin da yasa wasu ke ganin sam bai dace ba yayin da a gefe guda kuma wasu ke cewa sulhun alkhairi ne

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button