Uncategorized

Masha Allah Bayan Shafe Kwanaki cikin Mawuyacin Hali Daliban Nigeria Sun Sauka Lafiya Daga Sudan

Tun farko a yammacin Larabar ne hukumomin Najeriyar suka bayyana cewa jirgin na farko ya taso daga filin jirgin sama na birnin Aswan.

kashin farko na daliban kasar daga Sudan waɗanda ke guje wa yaki sun isa gida da talatainin dare, ranar Laraba.

Daliban wadanda suka sauka da misalin ƙarfe 11:30 na dare a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja na daga cikin kason farko da suka samu ficewa daga Sudan ta kasar Masar.

Jirage biyu ne dai suka sauka a daren na ranar Laraba, inda jirgin saman sojin ruwa na Najeriya ya ɗauko mutum 94, yayin da jirgin kamfanin AirPeace ya ɗauko mutum 283.

Hakan dai na zuwa ne sama da mako biyu bayan ɓarkewar faɗa a Khartoum, babban birnin Sudan.

Sudan ta fada cikin wani yanayi ne bayan fito-na-fito tsakanin bangarori biyu na mayaka a kasar.

Alkaluma daga hukuma sun bayyana cewa rayukan daruruwan mutane sun salwanta ya zuwa yanzu, sai dai babu sahihin bayani kan yawan wadanda suka mutun.

Kasashe da dama sun gaggauta wajen ganin sun kwashe ƴan kasarsu, sai dai Najeriya ta fuskanci tsaiko bayan ƙalubale da dama.

A ranar Laraba ne Birtaniya ta sanar da kammala kwashe ‘yan kasarta, a daidai lokacin da jirgi na farko da zai kwaso ‘yan Najeriya mazauna Sudan din ke shirin baro Masar.

Yanzu haka dai akwai sauran dubban ‘yan Najeriyar mazauna Sudan da suke jiran a kwaso su, wadanda galibi dalibai ne da ke karatu a jami’o’i daban-daban na kasar.

Baya ga ɗaliban da ake sa ran za su baro Sudan ɗin ta Masar, akwai wasu da ke a birnin Port Sudan, waɗanda ake sa ran za su tsallaka Saudiyya ta bahar Maliya kafin jirgi ya kwashe su daga Jiddah zuwa gida Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button