News

Video: Innalillahi Daya Daga cikin Motocin Daliban Nigeria Ta Kama da Wuta a Kan Hanya

Daya daga cikin motocin safa din da ke jigilar ‘yan Najeriya da suka makale daga Khartoum, babban birnin kasar Sudan, zuwa tashar jiragen ruwa ta Sudan wato Port Sudan, inda za’a dauke su zuwa kasar Saudiyya ta kama da wuta da sanyin safiyar ranar Litinin.

Motocin safa 26 ne dauke da ‘yan Najeriya da suka makale suka bar Al Razi da misalin karfe 12 na safiyar ranar Litinin zuwa Port Sudan.

Wakilinmu ya rawaito cewa, daya daga cikin motocin safa din da ke jigilar dalibai ‘yan Najeriya kimanin 50 daga kasar Sudan mai lamba (Katsina 1) da ke kan hanyar zuwa Port Sudan a wani bangare na zagaye na biyu na Gwamnatin Tarayyar Najeriya na kwashe ‘yan kasar, ta samu matsala saboda tsananin zafi da daya daga cikin tayoyin motar ta yi.

Shugaban kungiyar Dattawan Najeriya da ke kasar Sudan, Dokta Hashim Idris Na’Allah, na daya daga cikin fasinjojin da ke cikin motar safa din, wadda ke dauke da dalibai 50 da suka hada da maza 49 da mace 1.

Wannan lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 2:30 na safe agogon Sudan.

Direban ya tsayar da motar safa din a kusa da wani shigen bincike na dakarun RSF, kafin tayar motar ta fashe wanda ya yi sanadin tashin gobara.

Sai dai dukkan fasinjojin sun tsira ba tare da wani rauni ba.

An raba 40 daga cikin fasinjojin 50 ga sauran motacin safa din da ke kwashe daliban, yayin da sauran fasinjojin suka kwana inda lamarin ya faru tare da direban a shingen binciken dakarun RSF.

“Daliban sun ce da gaske dakarun RSF sun yi iya kokarinsu wajen taimaka wa fasinjojin tare da ba su kofunan shayi da safe kafin su tafi,” in ji Sani Aliyu da ke Sudan.

Tun daga lokacin suka ci gaba da tafiya zuwa Port Sudan.

Fiye da ‘yan Najeriya 1,000 ne aka kwashe su ta hanyar Port Sudan sakamakon matsalolin da aka fuskanta wajen wadanda aka kwashe na farko a kan iyakokin kasar Masar.

‘Yan Najeriya da suka makale sun shafe kwanaki biyar a kan iyakokin kasar yayin da jami’an Masar suka hana su shiga kasar, inda tuni jirage ke jiran kwashe su zuwa Najeriya.

Ga cikakken Video Yadda Lamarin ya Kasance.

https://youtu.be/iLy015zdLWE

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button