Kannywood News

MASHA ALLAH: Ku Tayani Da Addu’a Nasamu Juna Biyu A Cewar Tshohuwar Jarumar Kannywood Ummi Rahab

Ku Tayani Da Addu’a Nasamu Juna Biyu A Cewar Tshohuwar Jarumar Kannywood Ummi Rahab

Nà Samú Cíkí, Céwar Tsóhúwar Jarúmar Kannywóód Ummí Rahab

Matar mawaƙi, furodusa kuma jarumi Shu’aibu Ahmed Abbas (Lilin Baba) kuma tsohuwar jarumar Kannywood, Rahama Saleh Ahmed (Ummi Rahab), ta bayyana cewa ta samu ciki.

Ummi ta ba da wannan sanarwar ne a Instagram, inda ta wallafa hoton ta sanye da jar atamfa, ta na zaune a kan kujera ta na murmushi.

A saƙon, ta rubuta da Turanci da manyan baƙaƙe: “I’m pregnant”, wanda Mujallar Fim ta fassara da, “Na samu ciki”.

Jarumar mai ritaya ta yi kira ga masoyan ta da su taya ta murna, har ta yi alƙarin za ta ba da tukwicin katin waya ga mutum 50 na farko da su ka tura saƙon murnar a ƙasan hoton nata.

Hoton da Ummi Rahab ta wallafa tare da sanarwar ciki da ta samu Ta ce: “Idan na samu ‘comments’ ta hanyar rubuta ‘Congratulations’ a ƙarƙashin wannan hoton, zan ba da kyautan kati … ga mutane 50”.

Sai dai ba ta faɗi ko katin nawa ɗin za ta ba kowane mutum ba. Haka kuma matar ta Lilin Baba ba ta bayyana ko cikin nata ɗan wata nawa ne ba.

Ɗimbin masu bibiyar ta a Instagram sun taya ta murna tare da taya ta fatan alheri.

Ita dai Ummi, an ɗaura auren ta ne da Lilin Baba a ranar Asabar, 18 ga Yuni, 2022, a Tudun Murtala, Kano, a kan sadaki N200,000.

Jarumi Ali Nuhu, wanda shi ne waliyyin ango, shi ne ya karɓi auren.

Mé za kúcé

Copyright © Fìm Magazíne

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button