Kannywood News

Masha’Allah Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Ladan tare da Mijin ta Sunyi Murnar Cika Shekara tara da Yin Aure.

Masha’Allah Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Ladan tare da Mijin ta Sunyi Murnar Cika Shekara tara da Yin Aure.

Tsohuwar Jaruma a Masana’antar shirya Finafinan Hausa Fati ladan tayi Murnar Cika Shekara tara da Yin Aure ita da Mijinta Mai suna yarima shettima.

Fati ladan dai tana daya daga cikin jerin manyan jaruman Kannywood da sukayi tashe Matuka a baya, sannan kuna tana cikin jerin jarumai mata wanda Aurensu yayi Albarka.

An daura Aurenta a shekarar 2013 yau Kimanin Shekara 9 Kenan Hakan yasa Sukayi bikin murnar cika shekara 9 dayin aure.

Haka zalika tsohuwar jarumar na daga cikin jaruman da Auren Su ya dade batare da kalubale ba.

Ansha zargin Alakanta cewa, ba kasafai jaruman kannywood suka fiye zaman aure ba.

Duba da yadda ake ta ganin suna aure, amma daga bisani sai aji auren ya mutu, sun dawo harkar su ta film

Gadai hotuna da bidiyoyi da mijin nata ya wallafa a Shafin sa na Instagram.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button