News

Matashi Shamsuddeen a garin Zariya yayi ridda zuwa Kiristanci bisani har Sun bashi Mata.

Matashi Shamsuddeen a garin Zariya yayi ridda zuwa Kiristanci bisani har Sun bashi Mata.

Matashi Shamsu Hussaini Zariya yayi ridda zuwa Kiristanci har Sun bashi mata.

Shamsuddin Hussaini, matashi ne ɗan shekara 22 wadda ke Anguwan Alkali cikin garin zaria city. Bayan kasancewar shi ɗan musulmai jikan musulmai hakan bata hanashi canza addini ba inda ya zabi ya koma addinin kiristanci “Christianity.”

Watannin baya kaɗan Shamsu yayi tafiya inda ya shafe watanni bai dawo gida ba kwatsam sai a cikin yan kwanakin nan ya dawo inda ya tabbatar wa mutane cewa ya canza addini daga Musulunci zuwa kiristanci “Christianity.”

Duk dacewa bai bayyana dalilanshi ba amma akwai abubuwan da mukayi la’akari dasu wadda muna kyautata zaton sune sanadiyyar dayayiwa zabama kanshi wannan hanyar, dalilan kuwa sune kamar haka.

1, Matsi na rayuwa: Shamsu ya kasance maraya ne wadda babanshi ya rasu bai wuce shekara 1 da haihuwa ba hakan tasa yarasa duk wani gata da ɗa’a yake samu a wajen mahaifi.

2, Rashin kula daga yan uwan mahaifinsa: Shamsu ya fuskanci qalubale irin wadda maraya mare gata yake fuskanta. A halayya irin na mutanen yanzu idan mutum bai haifeka ba to kullun nisantanka yake tare da gujema duk wani bukatuwa naka inda hakan yasa koda kana aikata wani abu mare kyau kasancewar bai damu da halin da kake ciki to bazaisan kanayi ba balle ya gyara maka.

3, Neman mafita daga halin ƙuncin rayuwa: sau da dama yan addinin kiristanci (Christianity) sukanyi amfani da halin da mutum ke ciki domin su jawoshi garesu ta hanyar kyautata mashi. Tabbas a rayuwar yanzu sunfi musulmai tausayi dajin qai.

4, ƙarancin ilimin addini: tabbas ƙarancin ilimin addini ya taimaka wajen sauya addinin wannan yaron.

5, Halin ko’in kula na musulmai: tabbas musulmai mun nisanta daga faɗin Annabi S.A.W domin kuwa Annabi yana cewa duk wadda yasa maraya farin ciki ko ya kashewa mara ƙishi tabbas zai kashe mashi nashi qishin ranan alqiyama. dayawan marayu sunaji a zuciyarsu tamkar suba ya’ya ne kamar kowa ba domin kuwa suna rayuwa ne cikin Frustration.

MAFITA DAKUMA GUDUMMUWAR DA MUSULMAI ZASU IYA BAYARWA WAJEN DAWO DASHI MUSULUNCI

1, Akwai bukatan malamai su shiga lamarin suyi mashi da’awan dawowa addinin musulunci.

2, akwai bukatan bashi kulawa financially ta hakan zai fahimci cewa lallai shima ɗane kamar kowa kuma hakan zai ƙara mashi son musulunci a zuciyarshi.

3, samar mashi makarantar dazai koyi addini da samun ingantaccen ilimin sanin Allah mahalicci dakuma sanin addini.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button