News

Mutumin da yake batar da kama a matsayin mace ya hadu da fushin alkali

Mutumin da yake batar da kama a matsayin mace ya hadu da fushin alkali

Muhammad Abubakar dan asalin jihar Adamawa da yake yin basaja yana shiga ta irin kayan mata yana neman kudi a hannun mutane ya samu zama gidan gyaran hali..

Muhammed, wanda ya yi Diploma kan harkokin kasuwanci daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Adamawa, Yola, ya ce ya na yin ado kamar mace kuma ya na bin mata da sunan shi mace ne.

Muhammed wanda dan asalin garin Tashan Sani ne a karamar hukumar Yola ta Kudu kuma mai suna Fadi, ya bayyanawa wata babbar kotun majistare dake Girei kusa da babban birnin jihar Yola cewa, ya na aiki tare da abokansa mata.

Ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi ne bayan da dan sanda mai shigar da kara, Wamkai Ngapuro ya gurfanar da shi a gaban kotu.

An bayyana cewa bayan ya na samun kudi tsakanin Naira 500 zuwa Naira 1, 500, bisa la’akari da kudin da suke samu daga wurin maza a rana.

Babban Kotun Majistare, karkashin jagorancin Martina Gregory, bayan da ya amsa laifinsa, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan yari har zuwa ranar 5 ga Disamba, 2022.

Ko a watan da ya gabata sai da aka kama wani Saurayi a Kano wanda yake yawo da doguwar riga babu wando Idan ya hadu da mata sai ya daga rigar yana nuna musu al’aurar sa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button