![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/11/FB_IMG_1669131850169.jpg?resize=720%2C405&ssl=1)
Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un! Limamin Masallacin Quba da ke Madina, Sheikh Muhammad Abid Al-Sindi ya rasu.
Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu Yanzu Daga Shafin Dake Wallafa Labarai Dangane Da Abun Da Shafi Saudiya Wato Wato Haramin Sharifain Na Cewa.
![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/11/FB_IMG_1669130411110.jpg?resize=300%2C300&ssl=1)
Limamin Masallacin Quba da ke Madina, Sheikh Muhammad Abid Al-Sindi ya rasu.
A da dai wannan limami yana jagorantar Sallar tarawih ne a Masallacin Annabi kafin ya koma na Quba.
Shafin Twitter na Haramain Sharifain ne ya wallafa labarin rasuwar Sheikh Al-Sindi, inda ya kara da cewa tuni an yi jana’izarsa an kuma rufe shi a makabartar Baqee da ke garin Madinah.
Anan Muke Addu’a Ubangiji Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa Amin, Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani Amin Summa Amin