News

Nnamdi Kanu ya nemi a zauna lafiya tare da hakuri da juna a Najeriya.

Nnamdi Kanu Shugaban Biafra Wanda Gwamnati Ta Kama Ya Bukaci A Zauna Lafiya A Matsayin Kasa Daya

Shugaban kungiyar ‘yan tawayen nan ta (IPOB) masu rajin kafa gwamnatin Biafra.

Mazi Nnamdi Kanu, ya fara kira da hadin kai da kuma hakuri da juna a Najeriya daga can inda yake tsare a gidan gyaran hali.

Lauyan dake kare shugaban ‘yan tawayen, Aloy Ejimakor, shine ya bayyana hakan yau a shafin sa na Twitter.

inda yace “Ya shafe sa’o’i 4 tare da Namdi Kanu suna tattaunawa agidan gyaran hali.

“Kanu yana cikin farin ciki, yana mai neman a shawo kan wannan matsala nan bada dadewa ba.

Ya kuma jaddada muhimmancin hadin kai da hakuri da juna a dukkan bangarori.” Inji Lauyan sa Aloy Ejimakor.

Idan Ba’a Manta ba nnamdi Kanu Yasha furta kalaman dake nufin wargajewa.

Wanda yake tunzura Al’ummar kudu musamman ma inyamurai da kada su zauna a matsayin kasa Guda Da Hausawa.

Baya ga haka ya kirkiri wata kungiya mai suna ESN da nufin Amfani dasu wajen tada zaune tsaye.

Wanda daga bisani kungiyar ta dinga kai harw hare a ofisoshin yan sanda dakuma jami’an Soji.

Da Sunan yan bindigab da ba’a sani ba, Wanda sai daga bisani aka fara fahimtar cewar ESN ne ke aikata hakan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button