Religion

Ku Bada Fatun Layyar Ku Ga Kungiyar Izala Ta Kasa. Ibrahim Jalo Jalingo

Ku Bada Fatun Layyar Ku Ga Kungiyar Izala Ta Kasa. Ibrahim Jalo Jalingo

Kungiyar izala ta kasa tayi kira da a bata fatun layyar.

Kamar yadda mallam Ibrahim jalo jalingo ya wallafa a shafinsa na Facebook inda yake cewa.

1. Yau juma’a muna 6 ne ga watan Zul Hijjah, ke nan Talata mai zuwa ita ce ranar idin Layya.

Muna rokon Allah Ya nuna mana wannan babbar Rana lafiya, Ya kuma ba mu ikon yin ibadar Layya.

2. Kamar yadda aka sani ne cewa duk shekara Kungiyar Izalah ta Kasa na neman ‘Yan’uwa Musulmi da su ba da fatun layyarsu gare ta;

Domin cigaba da aiwatar da manyan ayyukan Da’awah da take yi a halin yanzu.

3. A wannan shekarar ma muna kiran Al’ummah a duk inda suke da su bayar da fatun layyarsu ga Uwar Kungiya ta Kasa.

Domin cigaba da manyan ayykan Da’awah da take yi.

4. Muna rokon Allah Ya taimake mu. Ameen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button