Psquare Ya Nuna Takaicinsa Kan Kabilanci Da Abinda Akayiwa Hausa A Kudu.

Fitaccen mawaki a Nigeria Peter okoye Mr P. Wanda Akafi Sani Da Psquare. Ya Nuna Takaicin Sa Kan Rikicin kabilanci dake faruwa a nigeria.

Kamar Yadda Mawakin Ya Wallafa a Shafinsa Na Sada Zumunta Inda Ya Bayyana Cewa Tabbas Shuwagabannin Nigeria Sun Gaza.

Psquare

Kuma Mawakin Ya Bayyana Takaicinsa Musamman Ma Akan Abinda Akayiwa Hausawa Mazauna Jahar Oyo A Kasuwar Shasha.

Mawakin Yayi Kira Da Akawo Karshen Rikicin Kabilanci A Nigeria.

Sannan mawakin Ya Bayyana Cewa “Shi Inyamuri ne Dake Auren Yoruba Kuma Girman Arewa Mazaunin Yankin Arewa Kuma Yayi Karatu A Arewa Kuma Ya Fara Samun Daukaka A Harkar Wakokinsa Ne Daga Arewa Kuma Yanzu Haka Ya Kan Iya Magana Da Yaren Hausa. Ya Kuma Yi Roko Dan Allah A Kawo Karshen Wariya Da Kabilanci A Nigeria.

Za’a iya cewa Psquare shine mawaki na farko a nigeria da yafara yin Allah wadai da irin wannan aika aikar.

Yankin na Arewa nada dimin mawaka mashurai da suka shahara a duniya. Amma har yanzu babu daya daga cikin mawakan yankin da ya fito yai Allah wadai da Abinda ya faru a jahar ta oyo.

Click Here To Drop Your Comment