Kannywood News

Rahama Sadau ta fara shirye-shiryen raba kayan azumi ga mabukata.

Fitacciyar Jarumar Shirya Fina Finan Hausa Rahama Sadau Na Shirin Bada Tallafin Kayan Abinci Ga Mabukata.

Kamar yadda aka sanine watan azumin ramadan wata ne mai falala da akeso mutane su yawaita kyauta ga mabukata

Kamar yadda kuke gani acikin hotonan nan Jaruma Rahama Sadau ta fara shirye-shiryen raba kayan azumi ga mabukata. Wannan shirin tana yin shi ne karkashin gidauniyar RayOfHopeN.

Ba wannan ne karo na farko da jarumar ke taimako irin wannan ba.

Duk da dai bata cika wallafa irin wannan abin alkhairan ba kuma bata fiye so ana yadawa a shafukan sada zumunta ba.

Jaruma rahama sadau nada wata gidauniya da take tallafawa marayu da gajiyayyu da marasa karfi mai suna rahama sadau foundation.

Hakazalika takwararta jaruma hadiza gabon ma nada tata gidauniyar tallafawa marasa karfi da gajiyayyu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button