An kama Abba Kyari da wasu ƴan sanda huɗu

Rahotanni daga Najeriya na cewa rundunar ƴan sandan ƙasar ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyari.

Rahotannin sun ce a yanzu haka ana tsare shi a sashin tattara bayanan sirri na rundunar dake Abuja.

Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan kasar ba ta fitar da sanarwa kan batun ba.

A ranar Litinin ne hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce tana neman ɗan sanda DCP Abba Kyari ruwa a jallo kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

A watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari mai muƙamin kwamishinan ‘yan sanda bisa zargin karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid – mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.

Click Here To Drop Your Comment