News

Sojojin Najeriya sun sami Gagarumar Nasara Na halaka, riƙaƙƙen ɗan fashin dajin da ya addabi Zamfara

Sojojin Najeriya sun sami Gagarumar Nasara Na halaka, riƙaƙƙen ɗan fashin dajin da ya addabi Zamfara

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka wasu riƙaƙun ƴan fashin daji biyu da suka addabi jihar Zamfara da maƙwabtatanta da suka haɗar da Kachalla Ruga da kuma Alhaji Auta.

Jaridar PrNigeria ta rawaito cewa mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne yayin luguden wutar jiragen sojin saman Najeriya a wasu dazuka da ke ƙauyen Gusami da kuma kauyen Tsamre a karamar hukumar Birnin Magaji.

Kafin mutuwarsu dai suna cikin gawurtattun ƴan fashin dajin da suka addabi arewa maso yammacin Najeriya.

Wasu majiyoyi sun ce an kuma hallaka yaransu da dama a lokacin hare-haren.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button