BA WANDA YA SAN GASKIYA SAI ALLAH

Wannan itace takardan shaidar bawa abokin Turji Musa Kamarawa mukamin SA a Gwamnatin Zamfara

Daga Datti Assalafy

Kamar yadda zaku gani, a kwanan wata, an bashi mukamin SA tun a ranar 26-9-2019

Watakila Gwamman Zamfara bai sani ba ya bawa maciyin amana abokin ‘dan ta’adda mukamin SA, ba wanda ya san gaskiya sai Allah

Lokacin da ‘yan sandan STS suka saki bidiyon Musa Kamarawa bayan sun kamashi, akwai wadanda suke ganin rashin dacewar a saki faifan bidiyon saboda sun jahilci aikin Intelligence

Amma na tabbata zuwa yanzu an fahimci hikima da dalilin da yasa ‘yan sandan suka saki bidiyon

Muna rokon Allah Ya bamu mafita na alheri

Click Here To Drop Your Comment