News

Wata Mata Tayiwa Kanta Da Kanta Yankan Rago A Jahar Kano

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wata mata da ake zargin ta kashe kanta a unguwar Sheka da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

‘Yan sandan dai sun ce matar ta kashe kanta ne ta hanyar amfani da wani fasasshen gilashin taga, inda ta yanka kanta bayan gartsa wa mahaifinta cizo sannan ta gutsire dan yatsanta da ke ciwo.

A cewar dan uwan marigayiyar mai suna Muhammad Sanusi, kafin ‘yar uwar tasu ta kashe kanta ta yi fama da ciwon yatsa wato karkare, wanda har sai da ta kai ga sun rufe ta a ɗaki na tsawon kwana biyar, sakamakon yadda ta koma tamkar mai taɓin hankali.

Ya ƙara da cewa a ranar da suka buɗe ta ne ta fasa gilashin tagar ɗakin da aka rufe ta sannan ta yanka kanta a makogoro.

A shekarar 2021 an samu mutane sama da biyar da suka kashe kansu a Kano da ke arewacin Najeriya, wanda wasu daga cikinsu aka alaƙanta da matsalar ƙwaƙwalwa.

Na baya-bayan da aka samu shi ne na wani matashi da ya kashe kan sa ta hanyar yanke al’aurar sa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button