Kannywood News

Tirqashi: Bani Da Buri Face Yana Su Gajeni A Harkar Film Cewar Ali Nuhu

Awata Hira da Akai dashi Jarumi, A Masana Antar Kannywood Ali Nuhu ya Shaidawa Duniya cewa Yafiso Yayansa Su Gajeshi A Cikin Sana’arsa ta Film. Kamar Yadda ya fada da bakinsa.

“Na so ƴaƴana su yi fim amma sai suka ƙi yarda”, Ali Nuhu.

Jarumin masana’antar finafinan Kannywood, Ali Nuhu ya bayyana yadda ƴaƴan sa suka ƙi zama jarumai a harkar fim.

Ali Nuhu ya ce burin sa ya ga ƴaƴan sa ana damawa da su a Kannywood, amma sai suka nuna akwai abinda suke son zama daban, ba harkar fim ba.

Jarumin ya ce bai damu ba, saboda yanzu zamani ya zo wanda ba a tilastawa yara abinda ake so su zama, a cewar sa goyon baya ake ba ƴaƴa akan duk abinda suke son zama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button