Kannywood News

TONAN SILILI: Wallahi Naziru Sarkin Waka Bai Turo Min Da Dubu 500 Gudummawar Gyaran Masallaci Ba, Cewar Comrd Nura Gready Bungudu

Wallahi Naziru Sarkin Waka Bai Turo Min Da Dubu 500 Gudummawar Gyaran Masallaci Ba, Cewar Comrd Nura Gready Bungudu

“Assalamu Alaikum RARIYA don Allah ku taimake ni na ga gidan jaridu da yawa sun wallafa cewa Naziru Sarkin Waka ya ba ni kuɗi kimanin naira dubu dari biyar domin a gyara wani masallaci kuma Wallahi ba gaskiya bane.

Daga baya an samu wasu mutane da ban san ko su wa bane sun kirkira Alart Ɗin karya cewa Naziru Sarkin Waka ya turo kudin, kuma Wallahi ba gaskiya bane.

Asali ma wajen kirkira alart din sun yi kuskure domin ba ni da alaka da bankin Access. Amman sun ɗauko lambar akawun dina wadda nake amfani da ita bankin Zenith sun rubuta Access Bank.

Kuma Wallahi Naziru Sarkin Waka bai san ni ba ni ma kuma ban san shi ba. Don haka ta yaya zai turo min kudi ba tare da yayi bincike ba haka kawai?

Don Allah ku taimake ni.”

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button