Rahotanni daga jahar anammbra na cewa tsagerun IPOB sun bankawa offishin yan sanda wuta jim kadan bayan nada sabon kwamishinan yan sandan jahar.

Lamarin da yai sanadiyar mutuwar jami’an yan sanda Guda Biyu A Jahar.

Kasa Da Kwana Daya Tal Da Nada Sabon Kwamishinan Yan Sandan Jahar Christopher Adetokumbo Owolabi, yan bindiga sunkai hari ofishin yan sanda tare da halaka yan sanda biyu Obosi a karamar hukumar Idemili a jihar.

Kamar yadda jaridar Daily trust ta rawaito yan bindigar sunkai farmakin ne da yammacin ranar laraba tare da sakin duk daurarrun dake ofishin tare da bankawa offishin wuta.

Click Here To Drop Your Comment