NewsReligion

Ba Haramun Bane Biyan Masu Garkuwa Da Mutane Kudin Fansa. Sheikh Ahmad Gumi.

Fitaccen malamin addinin musulimci sheikh ahmad mahmud gumi. Ya bada fatawarsa game da batun biyan yan bindiga masu garkuwa da mutane kudin fansa domin su saki wanda sukai garkuwa dashi.

Fatawar ta shehin malamin na zuwa ne kwanaki kadan bayan fatawar da sheikh ibrahim maqari ya bayar naganin haramcin biyan masu garkuwa da mutane kudi domin sakin mutumin da sukai garkuwa dashi din.

Farfesa ibrahim Maqari ya kafa hujja da Hadisin Manzon Allah (SAW) inda wani mutum ya tambayi manzon Allah S.A.W Cewa shin idan barawo ya bukaci ya kwace Masa kudadensa mai yakamata yayi, Sai Manzon Allah Mai Tsira Da Amince ya fada masa cewa kada ya bashi.

To Sai Dai Anasa bangarwn Sheikh Ahmad Gumi Cikin Tafsirin Alqur’ani Mai Girma da Ya gudanar a ranar Laraba a jihar Kaduna, Shehin Malamin ya bayyana cewa kuskure ne haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.

Inda Shima ya kafa hujja da Wani Hadisin Manzon Allah Tsira Da Aminci Su Tabbata A Gare Shi. da ya ce an yafewa mutum wasu abubuwa guda uku, daga ciki akwai abinda aka tilasta mutum yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button