News

An Kama Sojan Nigeria Dauke Da Harsasai Fiye Da Dubu Biyu 2000

Rahotanni Daga Maiduguri na cewa dubun wani soja ya cika bayan da aka kamashi da harsasai Fiye Da guda 2000.

Rundunar sojojin na tsimayin jami’in domin cigaba da bincike game da lamarin.

Jami’in mai suna sani muhammed an kamashi da akwati biyu na harsasai kamar yadda wanda suka tabbatar da lamarin suka shaidawa jaridar premium times.

Andai kama Sojan mai mukamin lance corporal, a tashar Maiduguri inda ma’aikatan NURTW suka kama shi lokacin da ya ke shirin hawa mota don Garzayawa babban birnin tarayya, Abuja.

Kamar yadda majiyar ta ruwaito cewa, sojan, wanda Yake acikin tawagar jami’ai na musamman A 198, an sallame shi daga aiki a Damasak da ke Jihar Borno bayan ya samu rahoton jinya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button