News

Wani Shugaban Ƙaramar Hukuma yayi abin azo a yaba ya ɗau nauyin yi wa yara 1,000 kaciya a Kano

Shugaban Ƙaramar Hukuma ya ɗau nauyin yi wa yara 1,000 kaciya a Kano

Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Habu Zakari, wanda a ka fi sani da Habu PA ya ɗau nauyin yi wa yara dubu ɗaya kaciya, ƴan Ƙaramar Hukumar.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Shugaban Karamar Hukumar ya gabatar da wannan shirin ne a wani ɓangare na cikar shekarar sa ɗaya a karagar mulki.

Ya ce ya yi hakan ne domin su ma yara su ji su kuma ga irin aiyukan da a ke yi wa alumma.

“Za mu ɗauki nauyin yin kaciyar a matsayin mu na shugabanni. Sannan kuma yara manyan gobe, suma su na da bukatar a yi musu wani abu da zai taɓa rayuwar su, ba wai manya kaɗai za a riƙa yi wa aiki ba.

“Shi ya sa mu ka ƙirkiro wannan shiri domin rage wa iyayen su nauyi,” in ji Zakari.

Ya kuma ce tuni an fara yi wa rukunin farko na yara 300 kaciyar, inda a ka baiwa kowa kaji guda 2 da kuma kuɗi Naira dubu 1.

Ya kuma tabbatar da cewa nan ba da daɗewa ba za a kammala yi wa dukkan yara dubu ɗayan da ya yi alƙawarin za a yi wa kaciyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button