Kannywood NewsNews

Yadda Aka Fara Shirya Fara Daukar Shirin Fim Din Haneefa. Yarinyar Da Malamin Makarantar Su Yai Garkuwa Tare Da Hallakata

Ƴan Kanywood za su shirya fim a kan Hanifa

Wani mai shirya fina-finan Hausa mai suna Ali Sa’id ya ce a wata mai zuwa ne zai fara shirya fim mai dogon zango mai taken “Hanifa” kan yarinyar da aka kashe a Kano.

BBC Hausa ta rawaito Ali Sa’id ya ce babban dalilinsu na yin fim din shi ne domin wayar da kan iyaye kan yadda za su saka ido kan yaransu bayan abin da ya faru da Hanifa.

“Muna kuma son a riƙa tunawa da Hanifa ta hanyar wannan fim ɗin” a cewar mai shirya fim din.

“Iyaye da dama sun nuna sha’awar wannan fim din kuma sun kawo yaransu domin fitowa a matsayin Hanifa a fim din,” in ji shi.

Idan za’a tuna a makonni baya ne dai Malamin su wata yarin mai suna Hanifa Abubakar ya sace ta kuma ya yi mata kisan gilla a Kano, lamarin da ya janyo cece-kuce a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button