News

A Gaggauce Anyi Kira Da A Dakar Da Yan Fim Din Hausa Daga Fara Daukar Shirin Fim Din Haneefa.

Anyi Kira Da A Dakar Da Yan Fim Din Hausa Daga Fara Daukar Shirin Fim Din Haneefa.

Daga Datti Assalafy

Kungiyar shirya fina-finan Hausa na Arewacin Nigeria (Kannywood) sun fitar da sanarwa cewa zasu shirya film mai nisan zango (series) akan Hanifa yarinyar da Malaminta na makarantar boko Abdulmalik yayi garkuwa da ita ya kashe ta

Jagoran shirya film din mai suna Ali Sa’id yace a watan biyu zai fara shirya film din Hanifa, yace dalilin shirya film din shine domin ya nuna wa iyaye hanyar da zasu kare ‘ya’yansu, sannan kuma a dinga tunawa da Hanifa, film din mai dogon zango ne, zai fito kashi-kashi.

Ba za’a rasa abin fadakarwa a wannan shirin film na Hanifa da ake son shiryawa ba, amma ta wani bangaren yana tattare da illoli da hatsari masu yawa da zai haifar a cikin al’ummah.

Idan masu kokarin shirya film din Hanifa suna son shiryawa ne da kyakkawar niyya na fadakarwa, to su duba abinda zai je ya dawo, domin kar abinda Abdulmalik ya aikata akan Hanifa ya zama abin koyi a gurin masu raunin imani da son zuciya

Watakila akwai matasa ko yara masu karamar kwakwalwa da suke son su koyi yadda ake garkuwa da mutane amma basu san yadda zasu koya ba, don haka kar film din Hanifa ya zama makaranta na koyar da yadda ake garkuwa da yara kanana har ma da manya.

Masu shirya fina-finai suna bada gudunmawa sosai a duniya wajen koyar da mutane aikata munanan laifuka da zummar cewa wai suna fadakarwa ne

Akwai fina-finan da suke koyar da dabanci, fashi da makami da sata, lalata da karuwanci, munanan dabi’u da shaye-shaye, rawa da waka, kisan kai, ta’addanci, rashin ladabi da sauran miyagun laifuka da sunan ana wa’azantarwa

Misali da Kudancin Nigeria, yankin kudu ya tsinci kansa a yawaitar kashe mutane a cire sassan jikinsu don yin tsafi, kuma matasa ke aikatawa, babu inda suka koya face a fina-finan Nollywood na kudancin Nigeria da suke yawan shirya fina-finai akan Money Rituals.

Kuma ko da film din Hanifa ba zai haifar da barna ba, ina ganin abinda aka yiwa Hanifa cin zarafi ne, keta haddi ne da ta’addanci mai taba zuciya da kuma tayar da hankali, bai kamata ya zama abin tunawa ga iyayenta da kuma sauran al’ummah ba

Muna jawo hankalin hukumar tace fina-finai na jihar Kano ta dauki matakin da ya dace

Muna rokon Allah Ya jikan Hanifa, Allah Ya sa ta ceci iyayenta ranar Hisabi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button