Religion

BIDIYO: Kafin Mahaifin Mu Ya Rasu Saida Yayiwa Wadanda Suka Harbe Shi Allah Ya Isa

BIDIYO: Kafin Mahaifin Mu Ya Rasu Saida Yayiwa Wadanda Suka Harbe Shi Allah Ya Isa

Mahaifinmu ya yi wa wadanda suka harbe shi ”Allah ya isa” kafin ya rasu, in ji Abdulrahman Albani.

Babban dan marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani Zaria Yace Mahaifin Su Ya Yafe Musu Baki Dayan Su.

A yau ne dai Shehin malamin ya cika shekara Takwas 8 Cif Cif da rasuwa.

Kafin Rasuwar Shehin Malamin, Ya Barwa Yaransa Wasiyar Cewa Suyi Karatu, Basu Da Wani Gatan Da Ya Wuce Karatu.

Kamar Yadda Zaku Gani Cikin Bidiyon Dake Kasa, Babban Dan Nasa Ya Cigaba Da Cewa, Sun Hadu Da Kalu Bale Masu Yawa Bayan Rasuwar Mahaifin Nasu.

Ya Kara Da Cewa, Abinda Ya Faru Na Karshe Shine, Su Kannan Sa Da Suke Tare Dashi Mahaifin Nasu.

Wanda Suna Cikin Mota Daya Da Albani Aka Tare Su, An Harbe Shi, Amma Dayake Da Akwai Kana Nan Yara Da Su Sun Kwanta.

Amma Wasu Ba’a Same Su Ba, Amma Daya Dake Rike Da Mahaifin Mu, Sai Yake Cewa Baba Ka Yafe Mana.

Sai Yace Ya Yafe Mana Gaba Daya, Kuma Yace Wadanda Suka Zalince Shi, Allah Ya Isa.

Bbc Hausa Ta Rawaito Cewa,Ya kara da cewa abin da yake yi musu dadi shi ne ganin irin abubuwan alherin da mahaifinsu ya bari na ilimi da dalibai da har yanzu suna koyar da abubuwan da suka koya daga gare shi.

Abdulrahman Muhammad Auwal ya ce maganarsa ta karsher da mahafinsa ita ce lokacin da ya je wurinsa yin bankwana zai koma makaranta.

“Sati daya kafin rasuwarsa na je na same shi na ce masa gobe za mu koma makaranta, ya yi mini addu’o’i; daga nan ne kuma bayan mun rabu, washegari na koma makaranta ranar Asabar kawuna ya kira ni… ya ce ga abin da ya faru, an kashe malam. A lokacin na yi kokari na fito da tsakar dare na samu mota na dawo daga makaranta,” a cewar Abua Huraira.

Ga Bidiyon Nan Ku Kalla

https://youtu.be/z9O4tIRQhhw

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button