News

Yadda na tsallake rijiya da baya a harin jirgin ƙasa — Jaruma Rahma Sadau

Yadda na tsallake rijiya da baya a harin jirgin ƙasa — Rahma Sadau

Shahararriyar jarumar masana’antar finafinai ta Kannywood, Rahama Sadau da ‘yan uwanta sun godewa Allah da ya raya ta ta tsallake rijiya da baya, daga harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ranar Litinin ne ƴan ta’adda suka kai hari kan jirgin ƙasa da ya taho zuwa Kaduna daga Abuja, Inda suka jefa bama-bamai da yin harbe-harbe, lamarin da ya sanya wasu fasinjojin su ka rasu, wasu su ka samu raunuka, inda da yawa kuma sun bata ba a gan su ba.

Sai dai kuma Sadau ta wallafa a shafin ta na twitter cewa an shirya za ta shiga jirgin tare da ‘yar uwarta amma su ka yi latti basu samu guri ba, amma kuma bayyana cewa ta na da abokai da su ka shiga cikin jirgin kuma wadanda harin ya rutsa da su.

Ta rubuta, “Ni da ‘yar uwata mun so kasance a cikin jirgin da aka kai hari a daren jiya amma muka rasa shi”. MUN RASA!!

Jarumar ta yi amfani da damar wajen baiwa magoya bayanta shawarar su karbi katin zabe na dindindin (PVC) da kuma tabbatar da kirga kuri’unsu.

“Mu (AREWA) mu muka kawo kanmu wannan halin, mun zabi Shugabannin yanzu don su Magance Mana Matsalar tsaron da ta addebe mu, Amma hakan taki samuwa, to don haka idan Muka mallaki katin zabe sai mu zabi Shugabanni na gari.

A yau, an jibge jami’an tsaro masu tarin yawa a filin wasa na MKO Abiola, na fahimci cewa Nijeriya tana iya yin Maganin Wannan matsalar, kawai sun zabi su yi watsi da mu ai ta kashemu, so ba ruwan su.

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button