News

Yadda Wani Matashi Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyar Sa, Ya Kuma Karya ƙafar Babansa A Katsina

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un Yadda Wani Matashi Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyar Sa, Ya Kuma Karya ƙafar Babansa A Katsina

Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu-Yanzu Daga Shafin Jaridar Alfijir Hausa, Daga Comrd Ibrahim Da’u Dayi Wanda Ke Cewa.

Wani matashi mai suna Najeeb Umar Shehu ya kashe kishiyar mahaifiyarsa Hajia Hasiya Galadima tare da karya kafar Mahaifinsa da taɓarya a Unguwar Goruba Road cikin birnin Katsina.

Yanzu haka Mahaifin Nasa, Alhaji Umar Shehu Balele, yana kwance a Asibitin koyarwa ta gwamnatin tarayya dake katsina a bangaren kula da kashi.

Ita kuma an yi Jana’izarta kamar yadda Addinin Musulunci Ya Tanada.

Anan Muke Addu’ar Ubangiji Allah Ya Jikanta Ya Gafarta Mata Amin, Shikuma Mahaifin Ubangiji Allah Ya Bashi Lafiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button