![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/07/FB_IMG_1657703048947.jpg?resize=720%2C405&ssl=1)
Yadda Wasu Matasan Musulmai Suka Yi Dawainiyar Jinyar Abokinsu Kirista Har Zuwa Lokacin Jana’izarsa Bayan Ya Mutu A Jos
Wasu Matasa Musulmai A Jahar Plateau Sunyi Dawainiyar Jinyar Abokin Su Kirista Mai Suna Issac Har Sai Da Rai Yai Halinsa.
![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/07/FB_IMG_1657702284769.jpg?resize=219%2C300&ssl=1)
Wannan matashi mai suna Isaac Adamu ya mutu a ranar 5 ga watan Yuli bayan fama da rashin lafiya. Mazaunin unguwar Dadin-Kowa ne dake garin Jos jihar Filato.
Tuni aka yi jana’izarsa a makabartar COCIN dake Kangang.
Saidai wani darasin dauka a mutuwar Isaac shine lokacin da yake kan jinya, abokansa wadanda yawanci musulmai ne sun kasance tare da shi a koda yaushe.
Sun dinga bada gudummawar kudin jinyarsa a asibiti, haka ma bayan mutuwar sa abokan nasa musulmai sun tallafawa mahaifinsa har aka kammala jana’izarsa.
Masu karatu wane darasi kuka dauka a wannan labarin?