NewsPolitics

Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Ayarin Motocin Gwamna Ganduje Na Jihar Kano

Wasu Ƴan bindiga sun hari ayarin motocin Mai Girma gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a kan hanyarsu ta komawa Kani daga jihar Zamfara.

kamar Yadda Kwamishinan Watsa labarai A jihar Kano Muhammad Garba ya tabbatar wa da BBC labarin, ya Kara Da cewa al’amarin ya faru ne a yau Laraba.

Sai dai Malam Muhammad ya ce abin bai shafi Gwamna Ganduje ba domin ba ya cikin tawagar a lokacin da lamarin ya faru, “amma ƴan bindigar sun harbi motoci biyu daga cikin ayarin.

“Sun harbi motar Hukumar Kula da Kare Afkuwar Hadurra ta Najeriya FRSC da ke yi wa ayarin jagora da kuma motar daukar marasa lafiya da ita ma ke yi wa ayarin rakiya,” a cewar kwamishinan.

Gwamna Ganduje na cikin tawagar gwamnan jihar Jigawa wanda tuni ayarinsu ya yi nisa a lokacin da lamarin ya faru in ji hukumomin jihar Kanon.

“Ƴan sandan tawagar Gwamna Ganduje sun yi musayar wuta sosai da maharan inda aka fatattake su suka koma,” in ji Malam Muhammad.

Wata majiya daga gidan gwamnatin jihar Kano ta ce lamarin ya faru ne bayan da tawagar ta bar birnin Gusau daidai iyakar jihar Zamfara da ta Katsina.

Tuni dai ayarin ya isa Kano bayan faruwar lamarin.

Ayarin gwamnonin Kano da Jigawan suna komawa jihohinsu ne bayan da suka halarci taron sauya sheƙar da gwamnan Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button