News

BIDIYO: Yan Kungiyar IPOB Biafra Sun Kashe Fjlani Takwas 8 A Kasuwar Shanu Dake Jahar Abia

Ƴan IPOB sun kashe Fulani 8 a kasuwar shanu a Abia

A ranar Talata ne wasu ƴan bindiga da a ke zargin ƴan haramtacciyar ƙungiyar masu Rajin Samar da Yankin Biafra, IPOB su ka kashe wasu Fulani 8 da su ke kasuwanci a kasuwar shanu da ke Omumauzor, Ƙaramar Hukumar Ukwa ta Kudu a Jihar Abia.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa da su ka kutsa kai cikin kasuwar, ƴan bindigar sun buɗe wuta a kan mai-uwa-da-wabi, in da su ka kashe mutum 8 su ka kuma raunata wasu da dama.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Eze Chikamanyo, ya tabbatar da harin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Kwamishinan ya baiyana kaɗuwarsa a kan harin, inda ya ce abin takaici ne.

Ya baiyana cewa gwamnatin jihar ta kaɗu matuƙa a kan abinda ya kira rashin imani na kashe mutane 8 da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ya kuma yi alla-wadai da harin, inda ya ƙara da cewa tuni gwamnatin jihar ta girke jami’an tsaro a yankin kasuwar domin kare sauran ƴan kasuwa a kasuwar da kuma mazauna garin.

Chikamanyo ya kuma ci alwashin cewa gwamnatin jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta gano da kuma hukunta waɗanda su ka aikata wannan ɗanyen aiki.


Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button