Kannywood News

YANZU-YANZU: Allah Yayiwa Fitaccen Daraktan Shirin Nan Mai Dogon Zango Wato Shirin Izzar So Rasuwa A Jahar Kano

YANZU-YANZU: Allah Yayiwa Fitaccen Daraktan Shirin Nan Mai Dogon Zango Wato Shirin Izzar So Rasuwa A Jahar Kano

Allah ya yiwa Nura Mustapha Waye Daraktan shirin Izzar So mai nisan zango rasuwa a safiyar yau Lahadi.

Rahotonni sun ce Mustapha Waye ya rasu a mutuwar fuj’a, ana sa ran za a yi jana’izarsa nan gaba a yau a birnin Kano.

Kamar Yadda Abokin Aikin Nasa Lawan Ahmad Ya Wallafa A Shafukan Sa Na Sada Zumunta Cewa, Innalillahi wainnailaihirrajiun

Allah Ya Karbi Rayuwar Nura Mustapha Waye Director IZZAR SO Za Ayi Zanaidarshi Karfe 11 Insha Allah, Allah Ya Yafe Masa Kurakuransa Amin, Allah Yasa Idan Tamu Tazo Mu Cika Da Imani Amin.

Kamar Yadda Zaku Kalla A Bidiyon Dake Kasa, Jarumin Izzar So Lawan Ahmad Shine Ya Sanar Da Rasuwar A Shafinsa Na Sada Zumunta.

Nura Mustapha Waye Yayi Fice Wajen Nuna Kauna Dakuma Soyayya Ga Fiyayyen Halitta Annabi S.A.W.

Haka Zalika Ko A Fims Din Da Yake Bada Umarni Yakan Yi Kokari Ya Nunawa Al’umma Ribar Soyayyar Annabi Kamar Yadda Yayi A Cikin Shirin Izzar So.

Tabbas Wannan Rasuwa Ta Taba Fitaccen Jarumin Izzar So Wato Lawan Ahmad Kwarai Dagaske.

Gadai Bidiyon Ku Kalla

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button