News

Yanzu Yanzu Hukuma Tafara Bincike Akan Dan Sandan Daya Bindige Abokin Aikinsa Har Lahira

Yanzu Yanzu Hukuma Tafara Bincike Akan Dan Sandan Daya Bindige Abokin Aikinsa Har Lahira

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wani jami`in ‘Dan Sanda ya rasa ran sa bayan da bindigar abokin aikin sa ta tashi inda ta harbe shi, wanda ya rasu sanadin harbin da bindigar tayi masa a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a unguwar Kurna a hanyar ‘Yan Sandan ta komawa jihar Katsina bayan sun kammala wani aiki da suka je yi jihar Kano.

Sifiritandan ‘Yan Sanda, Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda shine kakakin rundar a jihar Kano ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

“Akwai jami`an ‘Yan Sanda na jihar Katsina wanda suka zo aiki a nan jihar Kano, wanda kuma a unguwar Kurna suna cikin tafiya a motar su bindigar daya ta tashi inda kuma bayan ta tashi ta samu wani ‘Dan Sandan da yake cikin mota din, bayan wannan lamari an daukeshi da gaggawa an garzaya da shi asibiti inda likita ya tabbatar da cewa ya rasu,” in ji Kiyawa.

Yanzu haka dai wannan ‘Dan Sanda da bindigar sa ta tashi wanda ya yi sanadiyar harbin wannan ‘dayan, wanda ya yi sanadiyar ran sa, an kama shi yana hannu, kuma an fara gudanar da bincike a kan wannan zargi na kisan kai.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button