News

Yanzu-yanzu Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Tare Da Sheke Kan Jami’in Dan Sanda A Jahar Ribas

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari A ofishin yan sanda Dake Rumuji A karamar hukumar Emohua Ta jihar Ribas.

Kamar Yadda Jaridar DAILY POST ta samu Rahoton cewa sun fille kan jami’in su daya A yayin Kai harin.

‘Yan bindigar sun kai harin Ne tare da kashe wani dan sanda guda a wani shingen binciken ababan hawa a mahadar Ogbakiri da ke karamar hukumar.

Maharan sun kuma lalata shingen binciken ‘yan sanda na C4i da aka sake dawowa Dashi kwanan nan wanda ke kan layin Emohua A hanyar gabas ta yamma a Fatakwal.

An kai wadannan hare-hare ne da misalin karfe 10 na daren Juma’a, lokacin da dokar hana fita da gwamnatin jihar Ribas ta ayyana ta fara aiki.

Wata majiya, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce ‘yan bindigar sun fara harbi ne daga Aluu da ke karamar hukumar Ikwerre ta Jihar kafin su ci gaba zuwa inda suka nufa.

Har yanzu rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ribas ba ta ce komai ba game da batun har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

A cikin ‘yan kwanakin nan Jihar Ribas ta sha fuskantar jerin hare-hare a kan Jami’an tsaro a cikin jihar, wanda ya haifar da ayyana dokar hana fitar dare daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe a kullum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button