News

Yanzu-Yanzu: ‘Yan Bindiga Sun Tare Motar KTSTA, Sun Kashe Direban, Sun Tafi Da Fasinjojin

Yanzu-Yanzu: ‘Yan Bindiga Sun Tare Motar KTSTA, Sun Kashe Direban, Sun Tafi Da Fasinjojin

Yan bindiga sun tare motar KTSTA, sun kashe direban, sun tafi da fasinjoji.

Labarin da muke samu yana nuni ne da cewa wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun tare motar hukumar sufuri ta jihar Katsina, KTSTA a kan hanyar ta na zuwa Jibia da

Rana a ranar Lahadi.
Kamar yadda Katsina Post ta samu, yan bindigar sun kashe direban motar sannan kuma sun kwashe fasinjojin cikin motar da ba’a san yawan su ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Cikakken labarin na nan tafe…

A Wani Labari Na Daban Da Muka Samu na Daban Na Cewa..

“Innalillahi Wa’inna ilaihir Raji’un Allahuma Ajjurna Fi Musibatana Hazihi Akhlifna Khairan Minha…

Lahaula Wala Ƙuwwata Illa BilLah Hasbunallahu wa Ni’imal wakil, Ɓarayin daji sun tare hanyar Jibia ɗazu da Rana kata dai dai Garin Farun Bala suka harɓe Direba har Lahira sun raunata wasu da harbin Bindiga.

Aƙalla sun ƙwashe Mutane Goma Sha Shidda sun tafi dasu daji, masu raunin kuma an kaisu Babbar Asibitin Jibia domin karɓar Magani.

Allah ya kawo mana ƙarshen wannan Ibtila’in Amin”

Muhammad Aminu Kabir

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button