News

Yanzu-Yanzu ‘Yan sanda sun kama Bello Turji ‘likitan’ Bello Turji, da wasu 36.

‘Yan sanda sun kama Bello Turji ‘likitan’ Bello Turji, da wasu 36.

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta kama wani ma’aikacin lafiya, Abubakar Hashimu, wanda ya yi wa fitaccen sarkin ‘yan bindiga, Bello Turji magani, a lokacin da sojoji suka raunata shi a wani hari da suka kai shekaru uku da suka wuce.

Da yake jawabi ga manema labarai a Sokoto a ranar Litinin, Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda Wato Ahmed Zaki, ya ce.

Jaridar Daily Nigerian Ta Rawaito Cewa. An kama Mista Hashim ne tare da wasu Mutum 36. Wadanda ake zargin sun hada da Musa Kamarawa, Bammi Kiruwa, Zayyanu Abdullahi, Hardo Yunusa da Samuel Chinedu, da dai sauransu.

A cewar DIG, an kama mutanen ne tsakanin 20 ga watan Janairu zuwa 29 ga watan Janairu. “Tsakanin ranar 20 ga watan Janairu zuwa 29 ga watan Janairu, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta Operation Sahara Storm ta gano tare da kai samame sansanonin ‘yan bindigar da ke kananan hukumomin Illela, Rabah, Isa da Goronyo a jihar Sakkwato.

“A yayin gudanar da aikin, ‘yan sanda sun kama mutane akalla 37 da ake zargi a wurare daban-daban, an kuma gano wasu abubuwa da dama.

“Dukkan wadanda ake zargin suna da alaka da fitaccen shugaban kungiyar, Turji, kuma dukkansu sun amsa laifinsu na aikata laifin ta’addanci.

“Duk da haka, ana ci gaba da gudanar da bincike kan shari’o’insu kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike,” inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button