Ƙasar Saudiya Ta Cafke Ƴan Najeriya 20 Masu Ɗaga Hotunan Ƴan Siyasa A Ɗakin Ka’abah

Hukumomi a ƙasar Saudiyya, sun cafke mutane 20, da aka kama su na daga Hotunan Bola Tinubu da sauran wasu Ƴan siyasan Najeriya a gaban ɗakin Ka’aba, a cewar hukumomin za a hukuntasu.

Majiyar ta cigaba da cewa a yanzu haka suna hannun mahukunta ƙasar, ƙarƙashin kulawar askarawa domin gurfanar dasu gaban kotu tare da yanke masu hukunci dai-dai da abinda suka aikata, majiyar kuma ta cigaba da cewa babu shakka zasu kwashi kwashin su a hannu.

Majiyar mu ta kuma jiyo cewa, hukumomin sunce Sam baza su laminci ire-iren waɗannan abubuwan da ‘Ƴan Najeriya suke ba, domin yin wani abu na daban a cikin ƙasar su ba, domin kuwa wannan sabon wani abu ne dasu ba Susan da shi ba.”

DAGA Shafin Arewa Media

Click Here To Drop Your Comment