![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/03/Capture-2022-03-21-20.16.21.jpg?resize=780%2C470&ssl=1)
Ƴan Kwankwasiyya sun yi dandazo a wajen zaben shugabannin jam’iyar NNPP a Kano
Dubban yan Kwankwasiyya ne suka mamaye harabar wurin da Jam’iyyar NNPP Mai kayan marmari za ta gudanar da baban zabenta.
![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/03/FB_IMG_1647890137928.jpg?resize=300%2C225&ssl=1)
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa an tsara gudanar da zaben ne a cibiyar koyar da Sana’o’i ta sani Abacha wato Abacha Youth Center da ke kan hayar Madobi.
Ana sa ran Jam’iyyar za ta zabi shugabaninta a mataki daban daban ayau Litinin.
Sai dai abinda ke jan hankali a wurin taron shi ne yadda magoya bayan Kwankwasiyya suka mamaye wurin.
Wannan dai baya rasa nasaba da yadda ake ta rade-radin jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso zai koma cikin Jam’iyyar zuwa nan da ƙarshen watan Maris.
Idan za a iya tunawa dai tun a watan da ya gabata ne Jam’iyyar ta rushe shugabancinta, tare da kafa kwamitin riko.
A yau Litinin ne dai a ke gudanar da zaben shugabannin Jam’iyyar da kuma ake ganin yan Kwankwasiyya ne suka mamaye dukkanin mukaman da za a zaba.