News

BIDIYO: Ƴan Sanda sun cafke sojoji 2 da wasu mutane 3 sakamakon yi wa mai POS fashi da makami

Ƴan Sanda sun cafke sojoji 2 da wasu mutane 3 sakamakon yi wa mai POS fashi da makami

Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Borno ta cafke wasu mutane biyar, da su ka haɗa da sojoji biyu bisa zargin fashi da makami da kuma kisan kai.

 

Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, Abdu Umar ya shaida wa Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Laraba a Maiduguri cewa waɗanda a ke zargi sun yi wa wani mai shafin POS, Yusuf Usman fashi a kasuwar ƴan waya da ke Bulumkutu a ranar 6 ga watan Febrairu.

A cewar sa, a yayin fashin, waɗanda a ke zargin sun kashe wani mutum tare da raunata wani mutum daban.

Ya ce jami’an ƴan sanda sun cafke mutum uku da su ka haɗa da Mustapha Lawan, mai laƙabin Bakura Dantawaye, Abubakar Mohammed, mai laƙabin Bro Shagi da kuma wani Umar Ibrahim.

Kwamishinan ya ce waɗanda a ka kama ɗin sun amsa laifin su, inda su ka ambaci sunayen wasu sojoji biyu, lgogo Michael, da Pte Jibrin Adamu cewa su ma abokan aikata laifin su ne.

Umar ya ƙara da cewa an cafke su ma sojoji biyun a ranar Lahadi bayan da ƴan sanda suka shiga neman su, inda ya ƙara da cewa su ma sun amsa laifin su.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button