News

Ƴan Sanda sun kama mutane 4 bisa kisan wani mutum a kan naira 100 a Legas

Ƴan Sanda sun kama mutane 4 bisa kisan wani mutum a kan naira 100 a Legas

‘Yan sanda a jihar Legas sun kama wasu mutane huɗu da ake zargin sun yi wa wani David Imoh mai shekaru 38 kisan gilla a yankin Lekki Phase One a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamen ga NAN a jiya Lahadi.

“Al’amarin ya faru ne a ranar 12 ga Mayu, 2022. An kama mutane hudu a rana guda dangane da wannan aika-aika. Muna nan mu na neman na biyar ɗin da a yanzu haka ya tsere.

“Wanda aka kashe shine Sunday Imoh, mai shekara 38. Za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan an kama su. Za mu tabbatar da an zartas musu da hukunci domin ya zama izina ga wasu,”

A cewar SP Hundeyin, ba a yarda da kisan gilla a jihar Legas ba, inda ya gargadi jama’a da su kiyaye da hakan.

“Kada ku ɗauki doka a hannunku,” in ji shi.

NAN ta jiyo cewa wasu da ake zargin ƴam achaɓa ne da ke aiki a yankin Lekki Phase One su ka lakada wa mamacin dukan tsiya a kan naira 100.

An gano cewa rashin cika Naira ɗari ne ya haifar da rigima tsakanin Imoh da wani ɗan achaɓa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button