News

Alaqa Nanan Daram Wasu ‘yan haɗama ne ke ƙoƙarin lalata alaƙar Ganduje da Tinubu Gwamnatin Kano

Tun ranar Alhamis sautin muryar, wanda gwamnatin Kano ta ce “ƙirƙirarsa aka yi”, ya karaɗe shafukan zumunta, inda aka ji mutanen biyu na tattaunawa game da alaƙar Ganduje na jam’iyyar APC da Zaɓaɓɓen Shugaban Najeriya Bola Tinubu.

Gwamnatin Jihar Kano a arewacin Najeriya ta gargaɗi al’umma game da yunƙurin wasu da ta kira “mamugunta” kuma “‘yan haɗama” da ke yaɗa wani sautin kiran waya da aka ce na Gwamna Umar Ganduje ne da kuma Ibrahim Masari.

Cikin wata sanarwa da Kwamashinan Yaɗa Labarai na Kano Muhammad Garba ya fitar, gwamnatin ta ce “wasu ne da aka biya ke yunƙurin ɓata alaƙa tsakanin Ganduje da Tinubu”.

Suna magane kan ganawar da Tinubun ya yi da jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, a birnin Paris na Faransa cikin makon da ya gabata.

Ya ce: ” A bayyane take cewa wasu ne da ba sa son ganin daɗaɗɗiyar alaƙa tsakanin Ganduje da Tinubu, da kuma Masari ke amfani da wannan damar don cimma muradansu.

“Ba za mu bari wasu ‘yan haɗama su lalata haɗin kai tsakanin Tunubu da Ganduje ba.”

A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16 bayan ya yi nasara a zaɓen watan Fabarairu. Sai dai jam’iyyun adawa na ƙalubalantar sakamakon zaɓen a kotu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button