News

Allah Sarki Yaya da ƙaninsa sun rasu yayin ɗauko wayar salula da ta faɗa cikin masai a Kano

Yaya da ƙani sun rasu yayin ɗauko wayar salula da ta faɗa cikin masai a Kano

Wasu ƴan uwa guda biyu a jiya Lahadi sun rasa rayukansu a ƙoƙarin ɗauko wayar salula da ta faɗa cikin masai a Jihar Kano.

Rahotanni sun baiyana cewa mutum na farko, mai suna Haruna Abdullahi mai shekaru 30 da haihuwa, shi ya fara shiga cikin shaddar domin ya ɗauko wayarsa da ta faɗa.

Lamarin da ya afku ne a ƙauyen Aku da ke Ƙaramar Hukumar Gaya ta jihar.

Rahotanni sun baiyana cewa yayin da marigayi Abdullahi ya shiga shaddar domin dauko wayar ta sa, sai ya maƙale ya kasa fitowa, lamarin da ya riƙa neman a kawo masa agaji.

Shaidun gani da ido sun ce Abdullahi na cikin wannan halin ne sai yayansa, mai suna Adamu Danjimmai, mai shekaru 45, ya shiga masan domin ceto kanin nasa, inda shi ma ya maƙale, sai su ka rasu gaba ɗaya.

A cewar mai magana da yawun hukumar Kwana-kwana ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi PFSII, ya ce sun sami kiran gaggawa a ofishin su na Gaya da misalin karfe 7:15 na safe daga wani Ali Ahmad wanda ya sa suka garzaya wurin cikin gaggawa.

“Da isa wurin da misalin karfe 7:25 na safe, mutanenmu sun gano wasu mutane biyu da aka ruwaito ‘yan uwan ​​juna sun makale a cikin wani rami na shadda.”

“Shaidu da suka shaida idanunsu sun tabbatar da cewa wands ya rasu na farko ya shiga cikin ramin ne don dauko wayarsa da ta fada, yayin da dan uwansa da ya je ceto shi shima ya kasa fito wa har ta Allah ga kasance”.

Abdullahi ya tabbatar da cewa an fito da dukkan wadanda abin ya rutsa da su a sume kuma daga baya aka tabbatar sun mutu

Yayin da tuni aka mika gawarwakin ga Hakimin Kauyen Aku Adamu Isyaku domin binne su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button