News

ALLAHU AKBAR: An Kammala Aikin Masallacin Da Wani Jami’in Sojan Nijeriya Ya Soma Ginawa Kafin Ya Rasu

ALLAHU AKBAR: An Kammala Aikin Masallacin Da Wani Jami’in Sojan Nijeriya Ya Soma Ginawa Kafin Ya Rasu

Cikin Ikon Allah Yau Aka Gabatar Da Addu’ar Bude Masallacin Da Matashin Soja Mai Suna Shuaibu Gosker, Ya fara Ginawa, inda Kafin Ya Kammala Ginin Allah Yah Karbi Rayuwar Sa A Filin Daga.

Matashin Sojan Ya fara Gina Masallacin A Naton Arewa Tun Yana Raye A Filinsa Dake Tsohon Nguru Ward Dake Nguru Jihar Yobe.

Duk Da Zaman Shu’aibu Matashi A Gidan Soja Hakan Bai Hana Shi Tunawa Da Goben Saba A Lokacin Da Yake Raye.

Ya Zabi Ya Fara Yi wa Allah Hidima Da Dukiyar Sa Ta Hanyar Gina Masallaci Domin Al’ummar Musulmi Su dinga Yin Ibada A Cikin Sa, Duba Da Yanayin Anguwar Sabuwa Ce Kuma Ba Masallaci A Yankin.

Sojan Ya Rasu A Jihar Borno A Fagen Daga Da Boko Haram Domin Kare Al’umma Da Dukiyoyin Su A Ranar 18/12/2020.

Daga Bisani kafin Ya kammala Ginawar Allah Ya yi Masa Rasuwa.

Bayan Ya Rasu Aikin Ginin Ya Tsaya, Hakan Yasa Aka Nemi Taimakon Al’umma Domin A ƙara Sa Ginin, Alhamdulillahi A Yanzu Dai An Kammala Ginin Harma An Buɗe Masallacin An Fara Yin Sallah A Cikin Sa Yau.

Yan’uwa Mu sanya Wannan Bawan Allah Matashin Soja Cikin Addu’ar Mu Musamman A Wannan Wata Da Muke Ciki Mai Albarka Na Ramadan, Allah Yaji ƙansa Yayi Masa Rahama.

Allah Yah Sashi A Aljanna, Suma Sauran Mutane Da Suka Bayar Da Gudunmawar Su Wajen Kammala Wannan Ginin Masallaci Kama Daga Yan’uwan Sa Da Abokan Sa Da Sauran Al’umma, Allah Ya Saka Musu Da Alkhairi Ya Biya Musu Bukatun Su.

Hakika Rayuwar Wannan Matashin Sojan Tayi Albarka, Allah Ubangiji Yaji Kansa Da Rahama Yasa Wannan Aikin Alkairi Daya Kudirci Niyaryi Yah Zama Sanadin Shigar Sa Aljanna

Daga ABUBAKAR MUHAMMAD SHEHU

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button