Religion

Wata mage ta ja hankalin Duniya a Yayin da ta gabatar da Sallar Tarawili cikin jam’i.

Wata mage ta ja hankalin Duniya a Yayin da ta gabatar da Sallar Tarawili cikin jam’i.

Lamarin ya faru ne a ƙasar Algeriya, ana tsakiyar gabatar da sallar Tarawihi kwatsam sai ga wata mage inda tayi tsalle tare haye kafaɗar limamin a yayin da yake gabatar da karatun Alqur’ani cikin Muryar mai daɗi ta ratsa jiki.

Limamin bai yi ƙasa a gwiwa ba wajan tausasawa magen tare da shafa jikinta da nuna kauna da tausayi a gare ta.

Haka limamin yaci gaba da shafa jikinta, harma ta haye kafaɗar sa, daga ƙarshe ta sauka da kanta.

Tun bayan bayyanar vidion, lamarin ya ja hankalin al’ummar Duniya inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa.

An yabawa limamin matuƙa da ya fito su hoton musulunci na tausasawa hatta ga dabbobi.

Babban abin lura dai anan shine: musulunci addini ne na rahama da tausayi ba wai ga mutane ba, hatta ga dabbobi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button