NewsPolitics

An bankawa babbar Kotun Tarayya Wuta Dake Jihar Ebonyi

Wani Rahotanni daga jihar ebonyi dake kidancin nigeria na cewa wasu yan bindiga sun kona babbar kotun tarayya dake abakalaki babban birnin jahar.

Ginin kotun dake kusa da ofishin jam’iyyar PDP dake jahar kan babban hanyar Enugu/Abakaliki.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jahar Loveth Odah ta tabbatar da aukuwar lamarin kamar yadda wasu kafofin watsa labarai suka tabbatar.

Inda suka kara da cewa maharan sun yi amfani da bama-baman da aka hada da fetur wajen kona kotun.

Rahotanni sun ce wutar da ta tashi ta shafi dakin karatu dakuma dakin mai gadin kotun.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu wani rahoton na rasa rai ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button